6 Yuli 2026 - 21:33
Source: ABNA24
Thailand: An Gudanar da Taron Girmama Shahidin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci

An gudanar da taron girmama shahidin jagoran juyin juya halin Musulunci tare da halartar wasu masoya Ahlul-Bayt (a.s) da masu kaunar manufofin juyin juya halin Musulunci a Thailand.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: A wannan taron, jami'in al'adu na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Thailand, yana mai girmamawa jinjinawa jagora shahidi, ya bayyana shi a matsayin alamar daukaka, Gwagwarmaya, hadin kan al'ummar Musulunci da kare wadanda ake zalunta, yana mai nuni ga halartar miliyoyin mutanen Iran a jana'izar, ya bayyana wannan kasancewar a matsayin alama ta tabbatuwar amincin al'umma, hadin kan kasa da ci gaba da tafarkin shahidai.

Ya kuma jaddada wajabcin bayyana tunani d mahangar shahidin jagora ga matasa da kuma yaɗa al'adun neman adalci, sadaukarwa da gwagwarmaya.

Daga nan mahalarta, tare da rike hotunan jagora shahidi, tutar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da alluna masu taken "Dole ne a yunkura," sun shiga wani tattakin alamtawa, ta hanyar nuna hadin kai da aminci, sun jaddada ci gaba da tafarkin shahidai da kare manufofinsu.

Mahalarta a tsawon hanya, tare da shelanta taken girmama darajar shahidai, goyon bayan manufofin juyin juya halin Musulunci, kare al'ummomin da ake zalunta, da kuma yin Allah wadai da laifukan gwamnatin yahudawa, sun jaddada ci gaba da tafarkin jagora shahidi da kuma tabbatauwa da riko ga manufofin 'yanci, adalci da Gwagwarmaya.

…………………….

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha